Najeriya za ta kara karfafa hadin gwiwa da MDD a bangaren wadata kasa da abinci
2024-09-04 09:22:54 CMG Hausa
Najeriya ta bukaci kara kyautata tsarin hadin gwiwa da majalissar dinkin duniya, wato MDD domin samun dorewar shirye-shiryenta ta fuskar samar da wadataccen abinci a kasar.
Bukatar hakan ta fito ne daga bakin ministan ayyukan gona da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari jiya Talata, 3 ga wata lokacin da yake karbar bakuncin mataimakiyar sakataren janaral na majalissar dinkin duniya Hajiya Amina Muhammed a birnin Abuja. Ya ce yana da yakinin cewa ziyarar za ta bude wani sabon babin alaka tsakanin Najeriya da majalissar dinkin duniyar.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Sanata Abubakar Kyari ya ce, samun tallafin majalissar dinkin duniyar dai zai kara zaburar da kokarin gwamnatin Najeriya wajen tabbatar da ganin ta tsaya da kafafunta ta fuskar samar da abinci domin amfani a cikin gida da kuma fitarwa zuwa kasashen waje.
Ya ce, kyautata alakar hakika tana da muhimmanci domin ganin cewa an samu damar biyan bukatun dimbin al’ummar kasa da suke fuskantar kalubale wajen samun wadataccen abinci kuma mai inganci.
“Ya zama dole mu kara zage damtse kan harkar ilimi tare da saka jari sosai a kan harkar gona domin amfani da damarmakin dake cikin shirye-shiryen ci gaba na majalissar dinkin duniya.”
Da take jawabi, mataimakiyar sakatare-janaral na majalissar dinkin duniya Amina Muhammed ta ce, harkokin noma na fuskantar kalubale sosai daga irin abubuwan dake faruwa a kan iyakoki.
“Ban jima da dawowa daga kasashen Sudan da Chadi ba, mun ga irin wadannan kalubalen na kan iyakoki a kasar Chadi, inda ake da miliyoyin ’yan gudun hijira kuma hukumomi ke ta kokarin samar musu da abinci da sauran abubuwan kyautata rayuwa.”
Ta ce majalissar dinkin duniya ta shiga ka’in da na’in wajen aiwatar da tsare-tsaren da za su shawo kan matsalolin ’yan gudun hijira a Najeriya tare kuma da maganin matsalolin tsaro. (Garba Abdullahi Bagwai)