Sin ta raya dangantakar hadin gwiwa a fannin ikon mallakar fasaha tare da kasashe da yankunan duniya fiye da 80
2024-09-04 15:42:18 CMG Hausa
Hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta kasar Sin ta gudanar da taron manema labaru a yau Laraba, inda ta yi bayani game da hadin gwiwar ikon mallakar fasaha a tsakanin kasa da kasa.
Kasar Sin ta raya dangantakar hadin gwiwa a wannan fanni tare da kasashe da yankunan duniya fiye da 80, yawan yarjejeniyoyin hadin gwiwar da ake gudanarwa a yanzu haka ya zarce 200, ta hakan an kafa sabon tsarin hadin gwiwar ikon mallakar fasaha a tsakanin kasa da kasa dake shafar bangarori daban daban, da kasashen dake makwabtaka, da ma bangarori biyu. (Zainab Zhang)