logo

HAUSA

An kaddamar da shirin “Afirka a cikin fina-finai” zagaye na biyu

2024-09-04 15:38:01 CGTN Hausa

 

A ran 2 ga watan nan, CMG ta kaddamar da shirin “Afirka a cikin fina-finai” zagaye na biyu wato bikin nune-nunen fina-finai da sauran ayyuka a jami’ar koyon harsunan waje ta Beijing BFSU. An gayyato masu shirya fina-finai  daga Najeriya da Tanzaniya da Habasha da Benin da sauransu, wadanda za su baje kolin fina-finan su guda 10 a jami’o’in kasar ta Sin, ban da jami’ar BFSU, za kuma su kai ziyara a jami’ar koyar da ilmin watsa labarai ta kasar Sin da jami’ar nazarin harkokin sufuri ta birnin Xi’an da jami’ar Sichuan.

Ofisoshin jakadancin Sin dake kasashen Afirka daban-daban na goyon baya shirin nan. Jakadan Sin dake Najeriya Dun Hai ya ce, yana farin ciki da ganin an nuna fina-finai 3 daga Najeriya a jami’o’in kasar Sin, matakin da zai karawa matasa Sinawa sani da fahimtar al’adun Afirka, wadanda za su burge su da kuma samu karbuwa daga wajensu sosai. (Amina Xu)