logo

HAUSA

Dandalin Tsarin Abinci na Afirka ya bukaci kirkire-kirkire, saka hannun jari don samar da abinci

2024-09-04 11:18:13 CMG Hausa

A jiya Talata ne wakilan dake halartar taron dandalin tsarin samar da abinci na Afirka ko AFS a birnin Kigali na kasar Rwanda, suka yi kira da a kirkiro sabbin fasahohi cikin gaggawa, da saka hannun jari, da kuma samar da tallafi a matakin gwamnati don kawo sauyi a fannin noma da tabbatar da wadatar abinci a fadin nahiyar.

Taron mai taken "kirkira, hanzarta, da kuma daukaka," wanda ya jawo hankulan mahalarta sama da 5,000 da suka hada da masu tsara manufofi, da masu zuba jari a harkar noma, da masana ilimi, da kungiyoyin manoma, da wakilan kamfanoni masu zaman kansu, da matasa, ya mayar da hankali kan gaggauta sauyin tsarin abinci na Afirka. 

Da yake jawabi a gun taron, firaministan kasar Rwanda Edouard Ngirente, ya jaddada muhimmancin yin hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci, da kamfanoni masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki, don cimma tsarin samar da abinci mai dorewa. Ya bukaci gwamnatocin Afirka da su yi amfani da fasahohin zamani, da aiwatar da ayyukan noma da za su iya jure yanayi, da samar da tsarin da zai ba da tabbacin samun abinci mai kyau kuma mai gina jiki ga dukkan 'yan Afirka. (Mohammed Yahaya)