logo

HAUSA

Jiragen saman kasar Sin sun nuna bajinta a bikin nune-nunen jiragen sama na kasa da kasa karo na farko na kasar Masar

2024-09-04 11:13:24 CMG Hausa

An fara bikin nune-nunen jiragen sama na kasa da kasa na kasar Masar karo na farko a jiya Talata a filin jirgin saman arewacin kasar, inda kasashen Masar, Sin da wasu kasashe suka gabatar da jiragensu. 

Tashar talabijin ta Masar ta rawaito cewa, shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi ne ya kaddamar da bikin wanda aka fara a jiya Talata zuwa Alhamis a filin jirgin sama na El Alamein na kasa da kasa da ke El Dabaa, a gundumar Matrouh.

Rahoton ya ce, bikin ya janyo hankulan kamfanoni da hukumomi jiragen sama da na harkokin sararin samaniya sama da 300, da kuma hukumomin da abin ya shafa da ke wakiltar kasashe da yankuna kusan 100. Daga cikin mahalarta bikin akwai kamfanonin kasar Sin da dama, wadanda suka zo da nau’ikan jiragen sama daban-daban, ciki har da babban jirgin saman fasinja kirar Sin ko C919.

Ranar farkon bikin ta fara ne da nune-nunen jirgin saman soja na Silver Stars na Masar. Kazalika, jiragen saman sojoji na Sin, Amurka, Faransa, Italiya, Jamhuriyar Czech, Saudi Arabiya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Turkiye, da Indiya su ma sun gabatar da nune-nunensu, ciki har jirgin sama samfurin Y-20, wato babban jirgin saman dakon kaya kirar kasar Sin shi ma ya nuna bajinta. (Yahaya)