Xi Jinping ya gana da takwarorinsa na Senegal da Saliyo da Guinea Bissau da Tanzaniya da Zambiya, da shugaban Mozambique
2024-09-04 14:34:41 CGTN Hausa
Da safiyar yau, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye, wanda ke ziyarar aiki da halartar taron kolin dandalin tattauna kan hadin kan Sin da Afirka wato FOCAC, a nan birnin Beijing.
Xi ya nuna cewa, FOCAC ya zama abin koyi ga hadin gwiwar kasashe masu tasowa, wanda ke jagorantar hadin gwiwar da duniya ke yi da kasashen Afirka, kuma ya taka rawa ga shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. A matsayin kasar dake gudanar da jagorancin FOCAC karo na 4 tare da Sin, Senegal na taka rawar gani ga hadin kan Sin da Afirka. Sin na fatan kara hadin kai da kasar, cimma nasarar jagorantar taron, da gaggauta zamanintar da Sin da Afirka cikin hadin kai da kuma bude wani sabon babi na huldarsu.
A nasa bangare, Faye ya ce, Sin da Senegal sun cimma nasarar gudanar da ayyuka da dama cikin hadin gwiwa, lamarin da ya ciyar da bunkasuwar tattalin arziki da kyautatuwar al’ummar Senegal. An kafa FOCAC bisa tushen amincewa da juna da mutunta juna da daukar matakai mafi dacewa da cimma nasara mai armashi. Matakan da suka baiwa nahiyar Afirka damammakin samun bunkasuwar tattalin arziki da al’umma. Senegal na fatan kara hadin gwiwarta da Sin, da tabbatar da cimma nasara a FOCAC a wannan karo.
Kazalika, a wannan rana da safe, daya bayan daya ne Xi Jinping ya gana da shugaban Saliyo Julius Maada Bio da na Guinea Bissau Umaro Cissoko Embalo da kuma na Tanzaniya Samia Suluhu Hassan, kana da na Zambiya Hakainde Hichilema, da shugaban Mozambique Filipe Jacinto Nyusi da firaminstan kasar Habasha
Abiy Ahmed Ali
. Bugu da kari, Xi da shugabar Tanzaniya madam Samia Suluhu Hassan da shugaban Zambiya Mr. Hakainde Hichilema sun ganewa idanunsu kan yadda aka kulla “yarjejeniyar zamanintar da layin dogo dake hade Tanzaniya da Zambiya”. (Amina Xu)