logo

HAUSA

Hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin makamashi na da makoma mai haske

2024-09-04 19:33:27 CMG Hausa

A yayin taron manema labaran da aka yi a yau Laraba, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana cewa, dangane da hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin makamashi, cikin ‘yan shekarun nan, kasar Sin tana dukufa wajen zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu a wannan fanni ta hanyar mika fasahohi, da yin hadin gwiwa a shirye-shirye masu nasaba, da kuma ba da goyon baya ga sha’anin kudi, lamarin da ya ba da taimako ga kasashen Afirka wajen neman bunkasuwa mai inganci ta hanyar kare muhalli, ba kuma tare da fitar da iska mai gurbata muhalli mai yawa ba.

Dangane da hadin gwiwar Sin da Afirka kan aikin kare tsaro, Mao Ning ta bayyana cewa, zaman lafiya da kare tsaro shi ne muhimmin batu da za mu tattauna a dandalin FOCAC na wannan karo. Kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da kasashen Afirka, wajen aiwatar da shawarar kare tsaro ta duniya cikin hadin gwiwa, domin neman bunkasuwar kasa da kasa ta hanyar zaman lafiya.  (Mai Fassara: Maryam Yang)