Shugaba Xi Jinping da mai dakinsa sun shiryawa baki mahalarta taron FOCAC liyafar maraba
2024-09-04 19:10:06 CMG Hausa
Da yammacin yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da mai dakinsa Peng Liyuan, suka jagoranci liyafar maraba da zuwan manyan baki mahalarta taron tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ko FOCAC na 2024, a babban dakin taruwar jama’a dake birnin Beijing. Daga baya sun dauka hoto tare. (Saminu Alhassan)