logo

HAUSA

Hadin gwiwar Sin da Afirka ya samar da hanyar samun bunkasuwa da zamanantarwa tare

2024-09-04 07:17:00 CGTN Hausa

A cikin 'yan shekarun nan, bisa bin ka'idojin aiki da cikawa, da sakamako na hakika, da kyakkyawar yakini, hadin gwiwar Sin da Afirka na kara samun ci gaba cikin inganci, kuma ta fadada a fannoni daban-daban. Kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen ba da gudummawa ga ci gaban Afirka ta hanyar ginawa da gyara muhimman ababen more rayuwa kamar madatsun ruwa da tituna da asibitoci, wadanda suka karfafa dunkulewar yankin, da habaka cinikayya da masana'antu. Don haka, yawancin kasashen Afirka suna daraja hadin gwiwarsu da kasar Sin, saboda tana goyon bayan manufofinsu na ci gaba. A fannin kiwon lafiya, tallafin jinya na kasar Sin ya inganta samun damammaki da walwala ga yawancin kasashen Afirka. Haka ma, shirye-shiryen horar da ilimi da fasaha, irin su tallafin karatu da kafa cibiyoyin Confucius da na Luban da dai sauransu sun inganta jarin dan Adam tare da tallafawa ayyukan zamanantar da Afirka. A bisa wannan shimfidar ne, kuma cike da kwarin gwiwa muke cewa hadin gwiwar Sin da Afirka ya samar da hanyar samun bunkasuwa, da zamanantarwa tare.  

Idan muka zo fannin aikin gona ma a iya cewa hadin gwiwar Sin da Afirka ta ginu ne bisa himmatuwa, da mutunta juna da taimakon juna. Shirye-shiryen da suka hada da ba da taimakon fasaha, da bunkasa yankuna aikin gona sun haifar da sakamako mai muhimmanci. Wadannan yunkurin ba wai kawai suna kokarin samar da wadatar abinci ga al'ummomin Afirka ba, har ma suna inganta zamanantar da noma a nahiyar. Sabon nau'in irin shinkafa da aka tagwaita, ya zama kyakkyawar martani ga yunkurin samar da wadatar shinkafa ga kasashen Afirka. 

Yayin da birane ke saurin bunkasuwa kuma tsarin cinikayyar kayayyaki ke kara karko, mu a iya cewa hadin gwiwar Sin da Afirka ta riga ta zarce matsayin samar da ababen more rayuwa kawai, a nahiyar Afirka, har ma ta kai ga kamfanonin kasar Sin na kayayyakin yau da kullum da ma na tattalin arzikin dijital su ma sun shiga nahiyar. Rahoton hasashen tattalin arzikin shekarar 2024 na Bankin Raya Kasashen Afirka ya yi hasashen cewa matsakaicin ci gaban kasashen Afirka a shekarar 2024 zai kai kashi 3.7 cikin dari, da kuma kashi 4.3 a shekarar 2025. Hakan ya sanya kamfanonin sarrafa kayayyakin masarufi na kasar Sin suke ba da gudummawa ga kamfanonin nahiyar Afirka wajen ganin an cimma wannan hasashen ta hanyar hadin gwiwar samun moriyar juna. (Sanusi Chen, Mohammed Yaha, Saminu Alhassan)