Daukar mataki kan sauyin yanayi na da muhimmanci wajen kare muradun samun ci gaba a nahiyar Afrika
2024-09-03 10:45:01 CMG Hausa
Ministan kula da muhalli na kasar Zambia, Mike Mposha, ya ce mummunan tasirin sauyin yanayi ka iya zama tsaiko ga nasarar da nahiyar Afrika ta samu wajen cimma muradun ci gaba masu dorewa na MDD, idan ba a gaggauta daukar matakai ba.
Ministan ya ce matsanancin yanayi a nahiyar na karuwa, lamarin dake mummunan tasiri kan ci gaban tattalin arziki da zaman takewa, wanda ke bukatar daukin gaggawa domin kare nahiyar daga munanan matsalolin sauyin yanayi.
Mike Mposha wanda kuma shi ne mataimakin shugaba na 1 na taron dandalin ministocin Afrika kan yanayi, ya kara da cewa, karuwar zafi da na matakin ruwan teku da sauyawar yanayin zubar ruwa sama, dukkansu na bayar da gudunmuwa ga tabarbarewar matsalar yanayi, wanda ke kawo tsaiko ga ayyukan gona da wadatar abinci da ma yanayin rayuwa.
Ya ce taron ministoci kan yanayi na taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan kalubalen sauyin yanayi ta hanyar hadaddun dabaru na Afrika, wadanda ke mayar da hankali kan bunkasa hidimomin da bayanan da suka shafi yanayi da karfafa hadin gwiwa da bayar da horo, domin mara baya ga juriya da shiryawa tunkarar yanayi.
Ya ce aiwatar da dabarun, za ta inganta karfin nahiyar na bayar da gargadin wuri da magance matsalolin sauyin yanayi. (Fa’iza Mustapha)