Shugabannin kasashen Sin da Malawi sun gana a birnin Beijing
2024-09-03 15:55:39 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Talata ya gana da takwaransa na kasar Malawi Lazarus Chakwera, wanda ke ziyara a nan birnin Beijing domin halartar taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC na shekarar 2024.
Shugabannin kasashen biyu sun kuma sanar da daukaka alakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa huldar abota bisa manyan tsare-tsare.
Shugaba Xi ya ce, kasar Sin a shirye take ta zurfafa hadin gwiwar abota da Malawi daga sabon mataki don sa kaimi ga samun ci gaba tare da amfanar jama'arsu. (Yahaya)