Kasar Sin ta sanar da fara bincike kan karin harajin da Canada ta yi wa wasu kayayyakinta
2024-09-03 14:36:46 CMG Hausa
Kasar Sin za ta kaddamar da bincike kan wariyar da Canada ta nuna ta hanyar kara haraji kan motoci masu aiki da lantarki tare da kayayyakin tama da goran ruwa na kasar Sin.
Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin ta bayyana a yau Talata cewa, har ila yau, kasar Sin za ta kaddamar da bincike kan jibge kayayyakin tsiron rapeseed da sinadarai da ake shigowa da su kasar daga Canada. (Fa’iza Mustapha)