logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da ka’idojin inganta cinikayyar hidimomin tare da bude kofa

2024-09-03 12:53:50 CMG Hausa

Majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar da wasu jerin ka’idoji domin samar da ci gaba mai inganci a bangaren cinikayyar hidimomi tare da fadada bude kofa.

Ana sa ran ka’idojin da suka kunshi manyan ayyuka 20 a bangarori 5, za su gaggauta raya harkokin na’urori masu kwakwalwa da kirkirarriyar basira da harkoki masu kare muhalli a bangaren cinikayyar hidimomi a fadin kasar.

Har ila yau, ana sa ran za su fadada girma da inganci tare da karfafa cinikayyar hidimomi, domin bayar da gudunmawa ga gina budadden tsarin tattalin arziki a wani babban mataki a kasar Sin.

Ka’idojin sun yi tanadin cewa, ya zama wajibi a fadada tsarin kasuwar kasa da kasa da zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa a fannin cinikayyar hidimomi, yayin da za a inganta manufofi da matakan tallafawa kirkire-kirkire a kasar. 

A cewar ka’idojin, kasar Sin za ta samar da muhallin raya cinikayyar hidimomi domin inganta bude kofa da kirkire-kirkire da takara cikin adalci da tsari. (Fa’iza Mustapha)