An gudanar da taron ministoci na dandalin FOCAC karo na 9 a Beijing
2024-09-03 19:44:46 CMG Hausa
An gudanar da taron ministoci na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka karo na 9 yau Talata a nan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin.
Ministocin harkokin waje, da ministocin tattalin arziki na kasashen Afirka 53, da kuma wakilan kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU, da na kungiyoyin kasa da kasa sama da mutane 300 ne suka halarci taron. A yayin taron, an shirya harkoki a dukkan fannoni, gabanin taron kolin dandalin FOCAC da za a bude.
Cikin jawabinsa, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi imanin cewa, bisa kokarin da mambobin dandalin FOCAC suke yi tare, taron na wannan karo zai karfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, zai kuma kasance muhimmin mataki na hada kan kasashe masu tasowa, don su shiga halin zamanantar da kasashen su tare.
Haka kuma, ya jaddada cewa, kasar Sin tana tare da ‘yan uwanta na Afirka a ko da yaushe, za ta kuma ci gaba da nuna goyon bayanta ga nahiyar a kwamitin sulhu na MDD. (Mai Fassara: Maryam Yang)