logo

HAUSA

Afirka ta Kudu za ta bullo da wani sabon tsari na saukaka wa masu yawon bude ido daga Sin da Indiya

2024-09-03 13:56:27 CMG Hausa

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Afirka ta Kudu ta sanar a jiya Litinin cewa, za ta bullo da wani sabon tsarin gudanar da yawon bude ido na kasar ko TTOS a takaice, wanda zai fara aiki daga watan Janairun shekarar 2025, domin saukaka wa masu yawon bude ido daga kasashen Sin da Indiya.

A cikin sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce, za a cire tsauraran matakai sannan kuma za a inganta ayyukan ba da biza ga masu yawon bude ido daga kasashen da dole sai da biza za su shiga kasar, kamar kasashen Sin da Indiya.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Afirka ta Kudu Leon Schreiber ya bayyana a cikin sanarwar cewa, an bayar da wannan sanarwar ne a lokacin da shugaba Cyril Ramaphosa ke ziyarar aiki a kasar Sin, domin nuna da gaske gwamnatin kasar ta ke yi wajen bude damammakin da ke tattare da sha’anin yawon bude ido a kasar.

Sanarwar ta kara da cewa, za a wallafa ka’idojin TTOS nan ba da jimawa ba, da kuma bayanai kan yadda masu gudanar da ayyukan yawon bude ido za su gabatar da bukatar shiga tsarin a sashen TTOS gabanin kaddamar da shirin a watan Janairu mai zuwa. (Yahaya)