logo

HAUSA

Mataimakin shugaban kasar Sin ya gana da shugaban kasar Malawi

2024-09-03 11:29:11 CMG Hausa

Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng ya gana da shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera, wanda ya zo Beijing domin halartar taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka Ko FOCAC na shekarar 2024.

Han ya ce, kasar Sin a shirye take ta karfafa da zurfafa mu'amala da Malawi, da ci gaba da nuna goyon baya ga juna kan muhimman batutuwan da suka shafi moriyar juna, da zurfafa hadin gwiwar cin moriyar juna, don amfanar jama'ar kasashen biyu.

A nasa bangare kuwa, Chakwera ya ce, kwarewar kasar Sin ta fuskar bunkasa kasa, ta matukar baiwa kasar Malawi kwarin gwiwa mai muhimmanci, inda ya kara da cewa, kasashen biyu sun ci gajiyar dadadden abotansu, kuma suna mutunta juna, da yin hadin gwiwar samun moriyar juna. (Yahaya)