logo

HAUSA

Ciyayin da ake nomawa domin samar da sinadarin Artemisinin

2024-09-03 12:48:42 CMG Hausa


Nau’in ciyayin da ake nomawa a gundumar Rong’an da ke jihar Guangxi ta kudancin kasar Sin ke nan. Ana amfani da ciyayin ne wajen tace sinadarin Artemisinin, domin harhada magungunan yaki da cutar malariya. Gundumar Rong’an na daya daga cikin yankuna mafiya noman ciyayin a kasar Sin har da duniya baki daya, kuma sinadarin Artemisinin da ake samarwa a gundumar ya zarce ton 100 a shekara, wanda ya kai kimanin kaso 1/4 na gaba dayan sinadarin da ake samarwa a duniya.