Kasar Kenya za ta gudanar da baje kolin bunkasa huldar cinikayya tsakanin Sin da Afirka
2024-09-03 10:20:44 CMG Hausa
Mashirya baje kolin kayayyakin masana’antu na kasa da kasa na kasar Kenya karo na bakwai sun bayyana a jiya Litinin cewa, Kenya za ta karbi bakuncin baje kolin a mako mai zuwa, wanda ke da nufin bunkasa huldar dake tsakanin Sin da Afirka.
Darektan kula da baje kolin Kenya na Afripeak Gao Wei, ya shaidawa manema labarai a Nairobi babban birnin kasar Kenya cewa, taron na kwanaki uku da za a fara a ranar 12 ga watan Satumba, ya hada masu baje kolin kayayyaki sama da 200 daga kasashen Sin da Afirka, domin baje kolin sabbin kayayyaki.
Pius Rotich, babban manajan kula da harkokin zuba jari da ayyukan ci gaban kasuwanci a hukumar kula da zuba jari ta kasar Kenya, ya bayyana cewa, kasar Kenya za ta yi amfani da wannan baje kolin don jawo karin jarin kasar Sin, domin baiwa kasar damar zama cibiyar masana'antu ta Afirka. Ya kara da cewa, tuni dai kamfanonin masana'antu na kasar Sin sun taimaka wajen rage dogaron da Kenya ke yi kan kayayyakin masana'antu da kuma habaka fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.
Cynthia Kamau, darektar cibiyar kasuwanci da masana'antu ta kasar Kenya, ta ce baje kolin zai samar wa kasar damar haduwa da masana'antun kasar Sin masu kayayyaki sabbin kira da suka dace da bukatun gida. (Yahaya)