Sin na mai da hankali matuka wajen aiwatar da sakamakon FOCAC
2024-09-03 19:56:55 CMG Hausa
A yayin taron manema labaran da aka yi a yau Talata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi bayani game da yadda aka aiwatar da sakamakon da aka cimma, yayin taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka.
Ta ce, kasar Sin tana mai da hankali matuka ga aiwatar da sakamakon da aka cimma yayin dandalin FOCAC. Bisa kididdigar da ma’aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin ta fitar, daga watan Disamba na shekarar 2021 zuwa watan Yuli na shekarar 2024, darajar kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga kasashen Afirka ta kai dalar Amurka biliyan 305 da miliyan dari 9, inda Sin din ta cimma burinta a wannan fanni kafin isar wa’adin da aka tsara.
Haka kuma, a yayin da take tsokaci game da jita-jitar “kalubaloli daga kasar Sin”, wadda jami’an kwamitin musamman mai kula da harkokin kasar Sin na majalisar dokokin kasar Amurka suka yada, Mao Ning ta ce, kasar Sin na fatan ‘yan siyasar Amurka za su daidaita ra’ayoyinsu game bunkasuwar kasar Sin, su kuma daina haifar da sabani a tsakanin bangarorin biyu, gami da dakatar da rura wutar “sabon yakin cacar baki”. (Maryam)