Xi Jinping ya gana da shugaban AU da shugabannin Kenya da Chadi
2024-09-03 14:51:55 CGTN Hausa
Da safiyar yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kwamitin AU Moussa Faki Mahamat da shugaban kasar Kenya William Samoei Ruto da na Chadi Muhammat Idriss Déby, wadanda suke nan birnin Beijing don halartar taron kolin dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka.
Yayin ganawarsa da Moussa Faki Mahamat, Xi Jinping ya ce, Sin na goyon bayan AU ta kara taka rawa wajen gaggauta sha’anin sada zumunta tsakanin Sin da Afirka. Yana mai fatan amfani da zarafi mai kyau da dandalin ya samar, don ingiza ci gaban da Sin da AU suka samu a mabambantan bangarori da karawa aikin kafa kyakkyawar makomar al’umommin Sin da Afirka ta bai daya kwarin gwiwa zuwa wani sabon mataki.
A nasa bangare, Faki Mahamat ya ce, bangaren Afirka na nacewa ga manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, da marawa Sin baya wajen kare mudadunta. Ya ce Afirka kuma na fatan Sin za ta ci gaba da taka rawar gani wajen jagorantar aikin taimakawa zamanintar da nahiyar, da shimfida zaman lafiya da samun ci gaban duniya.
Yayin ganawarsa da shugaba Ruto, Xi Jinping ya ce, har kullum, Sin da Kenya suna sahun gaba a hadin gwiwarsu karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”, kuma sun kafa wasu manyan ayyukan tuntubar juna, wadanda suke taka rawa wajen bunkasa tattalin arziki da rayuwar al’umma, matakin da ya amfanawa al’umommin kasashen biyu.
A nasa bangare, William Ruto ya godewa taron da Sin ta shirya a wannan karo, wanda ya samar da babban zarafi ga hadin gwiwar Sin da Afirka. Ya ce Kenya na fatan amfani da damammaki masu kyau don kyautata huldar abota bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu nan gaba.
Ban da wannan kuma, yayin ganawar Xi da Déby, sun sanar da daga huldarsu zuwa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare. (Amina Xu)