An gudanar da taron manema labarai kan taron koli na FOCAC
2024-09-03 15:00:00 CGTN Hausa
A safiyar yau Talata, cibiyar yada labarai ta taron kolin dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka shekarar 2024 wato FOCAC ta gabatar da taron manema labarai, inda Liu Yuxi, wakilin gwamnatin Sin na musamman mai kula da harkokin Afirka, kana jakadan kasar kan harkokin FOCAC, ya yi bayani kan taron da ke tafe tare da amsa tambayoyin da aka yi masa.
Liu Yuxi ya ce, kasancewar taron mafi girma da zai samu halartar manyan jami’an kasashen waje mafiya yawa a shekarun baya-bayan nan. Taron na shirin zartas da sanarwa da shirin aiwatar da ayyukan dandalin, da zummar yayata manufofin Sin na sada zumunta da kasashen Afirka cikin sahihanci da gaskiya, da ra’ayin samun moriya mai dacewa da ruhin sada zumunta da hadin gwiwar Sin da Afirka.
A cewarsa, ana samun ci gaba mai armashi wajen kafa wannan dandalin, wanda ya zama alamar abin koyi ta hadin gwiwar bangarorin biyu, kuma ke jagorantar hadin gwiwar duniya da kasashen Afirka da zurfafa hadin gwiwar kasashe maso tasowa. (Amina Xu)