Shugaba Xi ya zanta da shugaban Najeriya
2024-09-03 19:15:15 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na Najeriya Bola Tinubu a yau Talata, yayin da shugaba Tinubu ya iso birnin Beijing domin halartar taron FOCAC na 2024, tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin.
Yayin zantawarsu, shugaba Xi Jinping ya ce Najeriya muhimmiyar kasa ce mai tasirin gaske a nahiyar Afirka, kuma kasa mai yawan al’umma da damar samun bunkasuwa. Ya ce a matsayin su na manyan kasashe masu tasowa, Sin da Najeriya za su ci gaba da karfafa hadin gwiwa bisa matsayin koli, wanda hakan zai sanya sabon kuzari ga dangantakar sassan biyu a sabon zamani, tare da jagorantar kasashen dake samu saurin ci gaba, da masu tasowa wajen gudanar da ayyuka tare.
A nasa bangare, shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya ce, kasarsa tana son zama abokiyar kasar Sin mafi girma a fannin hadin gwiwar cinikayya da zuba jari a nahiyar Afirka. Kana ana son ganin karin kamfanonin kasar Sin su zuba jari da karfafa huldar hadin gwiwa a fannonin aikin gona, da masana'antu, da makamashi, da dai sauransu a kasar Najeriya.
Shugabannin biyu sun sanar da daga matsayin huldar kasashensu zuwa abokantaka da ta shafi manyan tsare-tsare na dukkan fannoni. Bayan ganawar su, sun kuma ganewa idanun su bikin sanya hannu kan takardun bunkasa hadin gwiwar kasashen su.
Har ila yau a dai Talatar nan, shugaba Xi ya gana da shugabannin kasashen Mauritania, da Zimbabwe da karin wasu kasashen. (Saminu Alhassan)