Liu Zhujun: zuwa wurin da kasarmu ta fi bukatarmu
2024-09-02 21:30:01 CMG Hausa
Liu Zhujun, wadda ta taba karatu a fannin hasashen yanayi a jami’ar koyon ilmin noma ta arewa maso gabas, ta kuma halarci gasar yin kirkire-kirkire da raya sana’a iri daban daban, kuma ta sami lambobin yabo, a halin yanzu ta kasance mai sa ido a kasa a ofishin kula da yanayi na birnin Sansha a lardin Hainan dake kudancin kasar Sin. Masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku labari ne game da wannan baiwar Allah.
Liu Zhujun ta girma ne a birnin Daqing na lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin. A cewar ta, wurin da ya fi nisa da ta taba zuwa shi ne birnin Harbin na lardin su, inda ta yi karatu a jami’ar koyon ilmin noma na arewa maso gabas. Bisa shirin da iyayen ta suka yi mata, bayan ta kammala karatu a jami’a, za ta ci gaba da aiki da kuma zama a arewa maso gabashin kasar. Amma duk da haka, ta tsallaka kilomita 4485, ta isa yankin dake kudancin kasar Sin.
Liu Zhujun ta ce, zuwa wurin da kasarta ta fi bukatarta, wata manufa ce ta sana’ar da ta dauka a lokacin da ta shiga jami’a.
Ta kara da cewa, a cikin wani kwas game da ba da jagoranci kan aiki da aka tsara ga sabbin daliban jami’a, kalaman da malamin ya fada sun burge ta sosai. Malamin ya ce, “Aikin kula da yanayi yana da wahala, kuma ya zama dole a sa ido kan bayanai kan lokaci, da yin hasashe da gargadi kan yanayi mai tsanani iri daban-daban. A lokaci guda, ya zama dole a kyautata, da kuma inganta karfin tinkarar duk wani irin hadari na yanayi a kan lokaci daidai, bisa ga taron musamman da aka gudanar don magance bala’un na babbar iska, ambaliyar ruwa da ma fari. Lokacin gudanar da wannan aiki, wanda ke kan gaba wajen gudanar da ayyukan ceto kan bala’u, na haifar da nasarar kare rayuka da dukiyoyin jama’a, wannan ma’anar nasarar za ta zama abun dake karfafa muku gwiwa wajen fara son wannan aiki na kula da yanayi”.
Irin maganganu na malamin sun harzuka zuciyar Liu Zhujun. A wancan lokacin ne ta yanke shawarar zuwa wuraren da kasarta ta fi bukata bayan kammala karatunta a jami’a, don yin aiki a sahun gaba wajen tinkarar bala’u, da rage karfin bala'i, wanda ya rage yanayi mai dadi da take ciki, ta hanyar fara wani sabon salo na sana’arta.
Yayin da ake gab da kammala karatu a jami’a, wani kamfani dake karbar ma’aikata ya jawo hankalin Liu Zhujun, wanda shi ne ofishin kula da yanayi na birnin Sansha a lardin Hainan.
Ofishin kula da yanayi na Sansha yana tekun kudancin kasar Sin, wato wuri ne dake kudu maso kudancin kasar Sin, wanda ya kasance a kan iyakar kasa ta yankin teku. Idan ana son gudanar da aiki a nan, yana nufin ana bukatar zama a tsibirin har tsawon kwanaki 180 a ko wace shekara, kuma za a fuskanci hali mai tsanani kamar yanayi mai zafi sosai, da cin abinci mai gishiri sosai, da kuma fuskantar tartsatsi sakamakon hasken rana mai karfi. Baya ga haka, babu abinci, ruwan sha da sauransu a tsibirin, wadanda duk suna bukatar jigilar su da kuma kawo su ta jiragen ruwa daga sauran yankuna, don haka da zarar an yi guguwa a cikin ‘yan kwanaki a jere, watakila za a fuskanci matsalar karancin abinci da ruwan sha.
Liu Zhujun ta tambayi kanta, shin za ta iya yin irin wannan rayuwa? A wannan lokacin, ta tuna da kwas din ta na farko, da ma kalmomin malaminsu, “Lokacin da kowa da kowa ke kokarin neman samun wadata bisa zamanin yanzu, shin kuna da kwarin gwiwar zaben wata hanya ta daban, wato zuwa wuraren da kasarmu ta fi bukatar ku?” Liu Zhujun ta ba da amsa a cikin zuciyarta cewa, “A gani na, zan iya!”
Duk da fuskantar yanayi masu wahala za ta yi, amma tana son gwadawa. A yayin da take neman ra’ayin iyayenta, duk da cewa sun kasance cikin damuwa da rashin so, amma a karshe sun mutunta zabin da ta yi.
A shekarar 2022, bayan ta kammala karatu a jami’a, Liu Zhujun ta tafi birnin Sansha don soma aikinta na binciken yanayi. A nan ne ta gano cewa, wahalhalun da ake sha sun wuce yadda suke a tunaninta na da. Ga misali, wani abokin aikinta ba zato ba tsammani ya kamu da ciwon tsiro a ciki, a lokacin mahaukaciyar guguwa, saboda yanayin likitanci maras inganci, an bata lokaci da yawa kafin kai shi asibiti, har ma ya kusan rasa rayuwarsa bayan isar sa asibiti ta jirgi mai saukar ungulu. Wani abokin aikinta na daban kuma ya bar gida don yin wani aiki, jim kadan bayan haihuwar dansa da ’yarsa, lokacin da ya koma gida yaran sun yi ta yin kuka sosai kamar sun ga bako. Ban da wannan kuma, sakamakon guguwar iska da aka yi a tsibirin, sun gaza samun kayan abinci a tsawon kwanaki 43, domin samun karin sinadarin bitamin, kowa yana dibar kayan lambu na daji a tsibirin...
Liu Zhujun ta ce, ko da yake kowa ya sha wahala mai yawa, amma farin ciki, da jin dadi a ko da yaushe ke kasancewa a cikin zaman rayuwarsu. Ga misali, a lokacin manyan bukukuwa kamar bikin bazara, ba sa iya yin murnar bukukuwan tare da iyali sakamakon aiki. A wadannan lokutan, duk abokan aikin ta a tsibirin za su taru don murnar bukukuwan kamar yadda ake yi da iyali a gida. Liu Zhujun ta kara da cewa, yayin da take tafiya zuwa wasu tsibiran da babu mutane zaune a cikin su, don kiyaye kayan aiki na binciken yanayi, ko da yake tafiyar ba ta da wahala sosai, amma yayin da take tsayawa a saman fitilun dake jagora ga jiragen ruwa a tsibiran, don kallon muhalli mai ni’ima ita kadai, sai ta ji duk matsalolin da take fuskanta da wahalhalun da ta sha sun kasance ba komai ba a gare ta.
Tun lokacin da aka kafa ofishin kula da yanayi na birnin Sansha a shekarar 1957, komai wahalar da ake sha ba a taba rasa rana guda ba ta lura da yanayi a cikin shekaru sama da 60. “Tsayawa, mayar da hankali, girmama aiki, sadaukarwa”, sun kasance ruhin masu aikin binciken yanayi na ofishin. A cewar Liu Zhujun, mafi wahalar wurin da nake, zan fi jin dadi sakamakon rawar da nake takawa. Ta kuma yi sa’ar gudanar da aikin kula da yanayi a Shansha, za kuma ta ci gaba da ba da gudummowarta a wannan wuri da kasar ke bukatarta.