logo

HAUSA

Zanga-zanga ta barke a Isra’ila domin neman Netanyahu ya amince da yarjejeniyar sakin mutanen da aka yi garkuwa da su

2024-09-02 14:45:49 CMG Hausa

Daruruwan dubban Isra’ilawa ne suka fita zanga-zanga a fadin kasar a jiya Lahadi, suna neman firaminista Benjamin Netanyahu, ya cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Hamas tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.

Kimanin mutane 700,000 ne suka shiga zanga-zangar a manyan tituna da wurare a fadin kasar, inda 550,000 suka shiga zanga-zanga a babban birnin Tel Aviv.

An fara zanga-zangar ce daga safiyar jiya har zuwa dare, bayan rundunar sojin Isra’ila ta sanar da dawo da gawarwarki 6 na mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.

Zuwa yanzu, akwai mutane 101 da aka yi garkuwa da su a Gaza, kuma ana tsammanin rabi daga cikinsu sun mutu sakamakon hare-haren Hamas ko kuma bomaboman Isra’ila. (Fa’iza Mustapha)