Taron FOCAC zai bude sabon babin zumunci tsakanin al’ummun Sin da Afirka
2024-09-02 19:35:49 CMG Hausa
A yayin taron manema labarai da aka yi a yau Litinin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi tsokaci kan taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, wanda za a gudanar a birnin Beijing. Jami’ar ta ce kasar Sin da kasashen Afirka suna da makomar bai daya, kuma taron FOCAC da za a yi zai karfafa mu’amalar dake tsakanin al’ummun bangarorin biyu, gami da bude wani sabon babi na zumunci tsakanin al’ummomin Sin da na kasashen Afirka, ta yadda za a inganta bunkasuwar dangantaka a tsakanin sassan biyu, yayin da ake tabbatar da gina al’ummar Sin da Afirka mai makoma ta bai daya.
Game da zargin da majalisar gudanarwar kasar Amurka ta yi wa kasar Sin kan batun hakkin dan Adam a jihar Xinjiang ta Sin kuwa, Mao Ning ta ce, kasar Sin na fatan Amurka za ta daina tsoma baki cikin harkokin gidan ta, da kaucewa illata moriyar Sin bisa hujjar wani batu da ya shafi jihar Xinjiang ta Sin. (Mai Fassara: Maryam Yang)