Shugabannin Sin da Mali sun gana a Beijing
2024-09-02 16:07:22 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana a yau Litinin da takwaransa na Mali, Assimi Goita, wanda ya zo Beijing domin halartar taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika (FOCAC) na 2024.
Shugabannin biyu sun sanar da daukaka dangantakarsu zuwa abokan hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare.
Yayin taron, Xi Jinping ya ce a shirye Sin take ta inganta dadaddiyar abotarta da Mali da ci gaba da marawa juna baya da taimakawa iya karfinta, wajen raya tattalin arziki da zaman takewar al’ummar Mali. (Fa’iza Mustapha)