logo

HAUSA

Cinikayya tsakanin Sin da Afirka ta yi matukar bunkasa

2024-09-02 20:03:35 CMG Hausa

A shekarun baya bayan nan cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta yi matukar bunkasa, inda aka samu fadadar hada hadar shige da ficen hajoji tsakanin sassan biyu, kamar dai yadda alkaluman hukumar kwastam ta Sin suka nuna.

Alkaluman da aka fitar a Litinin din nan sun nuna cewa, daga shekarar 2000 zuwa 2023, darajar yawan cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka ta karu daga kasa da kudin Sin yuan biliyan 100, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 14.08, zuwa yuan tiriliyan 1.98, karuwar da ta kai ta a kalla kaso 17.2 bisa dari a duk shekara.

Kaza lika, alkaluman na hukumar kwastam ta Sin sun nuna yadda a tsakanin watannin Janairu da Yulin bana, cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka ta karu da kaso 5.5 bisa dari a shekara, zuwa kudin Sin yuan tiriliyan 1.19, adadin da ya kai matsayin koli a tarihi a wa’adin. (Saminu Alhassan)