Masanan Afirka na goyon bayan gaggauta hadin gwiwar Sin da Afirka
2024-09-02 10:39:16 CGTN Hausa
A yayin da taron kolin dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka, wato FOCAC a takaice ke karatowa, wasikar masanan kasashen Afirka 50 da shugaban kasar Sin Xin Jinping ya amsa, na samun karbuwa. Masana da dama na bayyana cewa, wasikar Xi ta kara musu kwarin gwiwa wajen hadin gwiwarsu da masanan Sin, don taka rawa wajen gaggauta hadin kan Sin da Afirka da raya dukkanin kasashe masu tasowa baki daya.
Tsohon jami’in diplomasiyya na Afirka ta kudu, kana farfesa mai daraja a jami’ar horar da malamai ta Zhejiang ta kasar Sin Gert Grobler, ya yi imani da cewa, masanan Afirka da Sin za su kara tuntubar juna da gudanar da bincike cikin hadin gwiwa karkashin goyon bayan Xi Jinping da shugabannin kasashen Afirka, matakin da zai taka rawa a bangaren bayar da ilmi don goyon bayan muradun bai daya na kasashe masu tasowa. Haka kuma zai samar da sharadi mai kyau ga huldar Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare. Ya kuma yi fatan za a samu ci gaba mai armashi yayin taron, da ma ingiza huldar bangarorin biyu zuwa wani sabon mataki.
Shi kuwa babban direktan mujallar “Africa-China Economy” ta kasar Najeriya, mai nazarin tattalin arzikin Afirka da Sin Mr. Ikenna Emewu ya bayyana farin cikin samun wasika daga Xi Jinping. A ganinsa wannan wasika ta nuna amincewa ga masanan Afirka 63 masu dukufa kan nazarin hadin gwiwar Sin da Afirka. Yana mai fatan kara ba da gudunmawarsu ga hadin gwiwar bangarorin biyu, inda ya ce zai yi iyakacin kokarin dukufa kan wannan aiki. (Amina Xu)