logo

HAUSA

Najeriya da kasar Indonisiya sun sanya hannu kan yarjejeniyar samar da man ja

2024-09-01 14:55:20 CMG Hausa

Najeriya da kasar Indonisiya sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin habaka sha’anin samar da man ja da kuma bunkasa kasuwancin sa.

Kungiyar ’yan kasuwa masu samar man ja ta Najeriya da takwarar ta ta kasar indonisyya ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar ranar juma`ar da ta gabata a birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Yayin bikin kulla yarjejeniyar, shugaban kungiyar ’yan kasuwa masu samar da manja na kasar Indonisiyya Mr. Addy Martono ya ce kasar Indonisiya na nema hanyoyin da za ta fadada kasuwancin kayayyakin da take samarwa kamar man ja da sauran su, kuma abun farin ciki kamar yadda ya fada Najeriya ta ba ta damar cimma wannan buri nata.

Ya kara jaddada aniyar kasar ta Indonisiyya na taimakawa Najeriya domin ta habaka kamfanonin ta na samar da man ja, da kuma kara kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

A nata jawabin yayin bikin mataimakiyar sakatare janaral na kungiyar ’yan kasuwa masu samar da man ja na kasar Indonisiyya Mrs Lolita Bangu ta ce Najeriya kasa ce dake da damarmakin da dama ga masu zuba jari, kamar yadda ta fada yarjejeniyar da aka kulla za ta bayar da damar karin yawan manjan da ake shigowa da shi Najeriya, kasancewar tana daya daga cikin kasashen da suke yawan bukatar man.

Da yake jawabi, shugaban kungiyar ’yan kasuwa masu samar da man ja na Najeriya, Ambasada Alphonsun Inyang, ya tabbatar da cewa yarjejeniyar za ta samarwa kananan manoman kwankwar man ja karin ilimi a game da yadda ake samar da man ja ta hanyar fasahohin zamani tare kuma da alfanun sa ta fuskar tattalin arziki.(Garba Abdullahi Bagwai )