Adadin zirga zirgar fasinjoji ta karu yayin makwannin lokacin zafi a Sin
2024-09-01 16:07:09 CMG Hausa
Kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin, ya ce ya zuwa ranar Juma’ar da ta gabata, adadin tafiya tafiye da aka yi ta jiragen kasa a kasar Sin, ya kai miliyan 872, a gabar da jama’a ke kara yawan tafiye tafiye na lokacin zafi a kasar, adadin da ya karu da kaso 6.2 bisa dari kan na makamancin lokaci na bara.
Wasu alkaluma da kamfanin ya fitar a jiya Asabar, sun nuna matsakaicin adadin tafiye tafiyen fasinjoji a kowace rana tsakanin ranar 1 ga watan Yuli da 30 ga watan Agustan da ya gabata ya kai miliyan 14.29.
Ana danganta karuwar tafiye tafiyen ne da zirga zirgar dalibai yayin hutun lokacin zafi, da tafiye tafiyen yawon bude ido, da ziyarar iyalai, wanda hakan ke sanyawa a samu karin zirga zirgar jiragen kasa.
A bana, lokaci mafi yawan tafiye tafiye na lokacin zafi a kasar Sin, shi ne tsakanin ranar 1 ga watan Yuli da 31 ga watan Agustan da ya gabata.
Wasu alkaluman na daban daga ma’aikatar sufuri ta kasar Sin sun nuna cewa, adadin tafiye tafiye tsakanin shiyyoyin kasar Sin cikin watanni 7 na farkon shekarar bana, ya kai biliyan 37.99, adadin da ya karu da kaso 6.6 bisa dari sama da na shekarar da ta gabata. (Saminu Alhassan)