Kayayyakin fasahar kiwon lafiya na Sin sun burge ma’aikatan lafiyar Ghana
2024-09-01 15:24:53 CMG Hausa
Ma’aikata da sauran masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya a kasar Ghana, sun jinjinawa ingancin kayayyakin fasahar kiwon lafiya na kasar Sin, wadanda aka baje kolin su yayin wani bikin nune nunen kayayyakin kiwon lafiya na yini uku, wanda ya gudana a kwanakin baya a birnin Accra na kasar Ghana.
Baje kolin, wanda wani kamfanin kasar Sin mai mazauni a Ghana ya shirya, na da nufin tallafawa kasashen yammacin Afirka da ikon farfado da ingancin kayayyakin da ake bukata a fannin kiwon lafiya.
Kamfanonin Sin masu samarwa, da masu cinikayyar kayayyakin na fasahohin kiwon lafiya da suka baje hajojin su yayin bikin, sun nuna kayayyakin yin gwaje gwaje a dakunan binciken lafiya, da na lura da hakora, da idanu, da fasahar tsira allurai jikin maras lafiya domin jinya, da kayan samar da iskar shaka ta marasa lafiya, da na binciken sassan jiki. Sauran sun hada da na sarrafa iskar oxygen, da na nazarin sassan jiki, da na farfado da marasa lafiya, inda kamfanonin suka gwada yadda kayayyakin suke aiki.
Da take tsokaci bayan ganewa idanun ta wadannan kayayyaki da aka baje, shugabar kungiyar masu magungunan gargajiya ta kasar Ghana Sandra Ashong, ta ce abubuwan da ta gani a wurin baje kolin sun yi matukar burge ta. Ta ce Sin ta samu babban ci gaba a fannin raya fasahohin kiwon lafiya.
Ashong ta kara da cewa, “Akwai babbar dama ta bunkasa hadin gwiwar cimma moriyar juna a wannan fanni tsakanin Sin da Ghana. Muna fatan samun shigowar karin wadannan fasahohi, da dabaru cikin kasar mu, domin bunkasa fannin kiwon lafiyar al’umma”. (Saminu Alhassan)