Za a wallafa makalar Xi kan horas da matasa a mujallar Quishi
2024-08-31 15:46:58 CMG Hausa
Za a wallafa makalar da Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya rubuta, a mujallar Qiushi bugu na 17 na bana.
Xi, wanda shi ne shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin koli na soja na kasar Sin, ya jaddada baiwa matasan wannan zamani masu nagarta kyakkyawar kulawa, da dabi’u masu kyau, da basira, da kuzarin jiki, da sanin ya kamata, da kwarewar aiki, wadanda za su ci gaba da bunkasa tsarin gurguzu da kuma ci gaban harkokin gurguzu.
Qiushi ita ce babbar mujalla ta kwamitin koli na JKS. (Yahaya)