Sin ta ba da rahoton gagarumin ci gaba a fannin kare halittun ruwa
2024-08-31 16:18:14 CMG Hausa
Ma'aikatar kula da muhalli da halittun ruwa ta kasar Sin ko MEE ta bayyana a jiya Juma’a cewa, kasar Sin ta samu ci gaba sosai wajen kiyaye muhallin halittun ruwa na muhimman kogunan kasar, tare da kyautata ingancin ruwan kasar a rabin farkon bana.
Wani jami'in MEE Huang Xiaozeng, ya shaida wa taron manema labarai cewa, adadin koguna na fadin kasar da ke da ingantacciyar ruwa ya kai kashi 89.4 a shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 1.5 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Huang ya kara da cewa, wannan adadi ya zarce manufar da aka tsara a cikin shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 14 wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, da kashi 4.4 cikin dari.
Daukar kogin Yangtze a matsayin misali, Huang ya ba da rahoton cewa, kashi 98.5 cikin dari na wuraren da ake sa ido a yankunan kogin sun samu kyakkyawan ingancin ruwa a shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 0.4 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.
Bugu da kari, adadin nau'ikan kifaye na asali da aka samu a cikin kogin Yangtze ya karu zuwa 227, sama da nau'ika 34 da ake da su a shekarar 2022. Yawan nau'in halittun ruwa da ake karewa a kasar ya karu zuwa 14 a shekarar 2023, wato karuwar uku idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. (Yahaya)