Jihar Katsina za ta hada karfi da kungiyar ECOWAS domin taimakawa talakawa masu karamin karfi dake jihar
2024-08-31 15:04:55 CMG Hausa
Gwamnatin jihar Katsina dake arewa maso yammacin Najeriya ta kammala shirye shiryen hada karfi da kungiyar ECOWAS domin cin gajiyar shirin samar da abinci na kungiyar na tallafawa talakawa dubu 14,694.
Gwamnan jihar Dr. Dikko Radda ne ya tabbatar da hakan ranar juma’a 30 ga wata a birnin Katsina lokacin da yake kaddamar da kashi na biyu na shirin a Birnin Katsina,inda ya ce an tsara shirin ne domin rage kalubalen da masu karamin karfi musamman wadanda tashe -tashen hankula ya yi sanadin kauracewa muhallan su.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Gwamnan na jihar Katsina wanda ya zayyana tsare-tsaren da gwamantin jihar ta bijiro da su da zumma rage radadin rayuwa ga talakawa masu karamin karfi, ya ce jihar Katsina a halin yanzu tana daya daga cikin jahohi kalilan da suke amfani da tsarin gwamnatin tarayyar wajen taimakawa mutanen da suke cikin matsanancin yanayin rayuwa ta hanyar kafa hukumar saka jari da tallafawa rayuwar al’umma.
Dr Umar Dikko Radda ya kuma jaddada kudirin gwammatin jihar wajen taimakawa mutanen da suka gamu da matsalar hare-haren `yan ta`adda da barayin shanu da kuma masu garkuwa da mutane, haka kuma gwamnatin ta samar da shirye shirye na musamman na tallafawa zaurawa da suka rasa mazajen su sakamakon hare-haren `yan ta`adda.
A nasa jawabin, babban sakatare a ma`aikatar ayyukan jin kai da yaki da talauci na Najeriya Mr Abel Enitan ya ce adadin mabukata dubu 14,694 ne da suka fito daga jahohin Katsina da Sakkwato za su amfana daga kashi na biyu na shirin.
Shi ma da yake nasa jawabin, wakilin hukumar gudanarwar kungiyar ECOWAS a Najeriya Ambasador Nuhu Musa ya bayyana cewa shirin samar da abinci na duniya daya ne daga cikin shirye shiryen da kungiyar ta ECOWAS ta bullo da su wadanda suke da mutukar tasirin gaske ga kyautatuwar yanayin rayuwar al`umma baya ga tallafin da take bayarwa a fagen kiwon lafiya, ilimi da samar da ababen more rayuwa ga al`umomin mambobin kasashen kungiyar ECOWAS. (Garba Abdullahi Bagwai)