logo

HAUSA

Shugaban Afirka Ta Tsakiya: Karin kasashen Afirka suna son zurfafa hadin gwiwa da Sin

2024-08-31 16:23:01 CMG Hausa

Shugaban kasar Afirka Ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra ya bayyana wa wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG a birnin Bangui, babban birnin kasar Afirka Ta Tsakiya a kwanakin baya cewa, a halin yanzu, karin kasashen Afirka suna son zurfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin.

Shugaba Touadéra ya bayyana cewa, hadin gwiwa a tsakanin Afirka da Sin na da dogon tarihi, kuma bisa tushen yanayin bangarorin biyu da girmama juna kan ikon mallakar kasa da kuma ka’idojin samun moriyar juna. Sahihancin hadin gwiwarsu ya bayyana a zahiri, kana ana cike da sada zumunci da zama ‘yan uwa yayin da ake gudanar da ayyukan hadin gwiwa a tsakanin juna.

Game da kiran samun ci gaban duniya, da kiran kiyaye tsaron duniya, da kiran kiyaye al’adun duniya da sauran batutuwan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, shugaba Touadéra ya bayyana cewa, kasar Afirka Ta Tsakiya a shirye take ta ci gaba da yin hadin gwiwa da nuna goyon baya ga juna a tsakaninta da kasar Sin kan batutuwa daban daban. Kasarsa za ta aiwatar da jerin kiran da shugaba Xi Jinping ya gabatar, da zurfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin.

Hakazalika kuma, shugaba Touadéra yana begen taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC na wannan karo da za a gudanar a birnin Beijing. (Zainab Zhang)