logo

HAUSA

Wakilin Sin ya bukaci Amurka da ta yi kokarin sa kaimi ga tattaunawar zaman lafiya kan batun Ukraine

2024-08-31 15:22:32 CMG Hausa

A jiya Juma’a ne mataimakin wakilin kasar Sin a majalisar dinkin duniya Geng Shuang, ya bukaci kasar Amurka da ta yi kokari na hakika wajen sa kaimi ga tattaunawar zaman lafiya, da sassauta rikicin Ukraine. 

Geng ya bayyana hakan ne a taron kwamitin sulhu na MDD kan samar da makamai ga kasar Ukraine, a cikin martaninsa ga wakilin Amurka, inda ya ce, “Game da batun Ukraine, maimakon zafafan kalamai, kamata ya yi Amurka ta yi kokarin sa kaimi ga tattaunawar zaman lafiya da sassauta rikicin.”

Ya kuma ce furucin da wakilin na Amurka ya yi “wani abu ne da muka sha ji a baya ba tare da wani sabon abu a ciki ba”, wakilin ya yi kira ga bangaren Amurka da ya daina wasan nuna yatsa a cikin wannan zauren.

Geng ya ce, babban aikin gaggawa ga kasashen duniya a halin yanzu shi ne sa kaimi ga tsagaita bude wuta don dakatar da yaki da tabbatar da zaman lafiya, kuma kasar Sin ta yi ta tofa albarkacin bakinta kan batun zaman lafiya tare da yin kira da a yi kokarin kawo karshen wannan rikici.

Duk da haka, ba wai kawai rufe ido da kunnen uwar shegu Amurka ta yi ga kokarin da kasar Sin ke yi na samar da zaman lafiya ba, har ma ta ci gaba da yada karairayi a cikin kwamitin sulhu da kuma bata wa kasar Sin suna a kan batun Ukraine, wanda kasar Sin ke matukar adawa da hakan, kuma ba za ta amince da hakan ba, a cewar Geng. (Yahaya)