Xi: Sin da Afirka a ko da yaushe al'umma ce mai makomar bai daya
2024-08-30 19:35:17 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada a yau Laraba a cikin amsar wasikar da ya bayar ga masana daga kasashen Afirka 50 cewa, a ko da yaushe kasar Sin da Afirka al’umma ce mai makomar bai daya.
A cikin wasikar, Xi ya bayyana cewa, a yayin da ake fuskantar wani yanayi mai cike da rudani da sarkakiya a duniya, Sin da Afirka na bukatar karfafa hadin kai da hadin gwiwa fiye da kowane lokaci.
Xi ya kara da cewa, yana fatan masana za su kara yin binkice kan hanyoyin samun ci gaba na kasashe masu tasowa, da hadin gwiwar Sin da Afirka, da ma kasashe masu tasowa, da kuma ci gaba da ba da muhimmiyar goyon baya ta ilimi don gina al’ummar Sin da Afirka a babban matsayi kuma mai makomar bai daya da kare muradun kasashe masu tasowa.
A kwanan nan ne dai, sama da masana 60 daga kasashen Afirka 50 suka aike da wasika tare zuwa ga shugaba Xi, inda suka yaba da manyan nasarorin da aka samu a dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka. Yayin da suka bayyana fatansu cewa, wannan taron dandalin da ke tafe zai rubuta wani sabon babi na gina al'umma mai makomar bai daya ga Sin da Afirka. (Yahaya)