logo

HAUSA

Za a gudanar da taron ‘yan kasuwa na Sin da Afirka karo na 8 a Beijing

2024-08-30 14:19:48 CGTN Hausa

 

Mai magana da yawun kungiyar bunkasa ciniki ta kasar Sin Wang Linjie ta bayyana a gun wani taron manema labarai cewa, za a gudanar da taron ‘yan kasuwan Sin da Afirka karo na 8 a nan birnin Beijing a ran 6 ga wata mai zuwa, taron da zai kasance wani muhimmin sashi na taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na shekarar 2024.

Kungiyar bunkasa ciniki ta Sin da ma’aikatar kasuwanci ta Sin ne suka shirya gudanar da taron, wanda ya kasance mafi muhimmanci a bangaren masana’antu da kasuwanci tsakanin Sin da Afirka, dake karkashin tsarin dandalin FOCAC.

A gun taron manema labarai, Wang Linjie ta ce, masana’antu da kasuwanci wani muhimmin bangare ne na sada zumunci da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, kuma Sin ta kasance abokiyar ciniki mafi girma ga nahiyar Afirka a shekaru 15 a jere, kazalika Afrika ita ce ke kan matsayi na biyu ga kasar Sin a fannin ayyukan gine-gine a ketare. Ya zuwa yanzu, kamfanoni da kungiyoyi da kuma hukumomi 408 daga kasashen Afirka 48 sun yi rajistar halartar taron.

Tun bayan da aka kaddamar da wannan taro a shekarar 2003, a kan gudanar da shi a shekaru uku uku a kasar Sin da kasashen Afirka, kuma zuwa yanzu an gudanar da taron har sau 7. (Amina Xu)