logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Gombe ta bullo da shirin koyawa mata dabarun noman dankali a cikin gida

2024-08-30 10:49:55 CMG Hausa

Adadin mata 200 ne gwamnatin jihar Gombe ta fara baiwa horo a kan dabarun noman dankali da sauran kayan abinci a cikin gida, ba tare da zuwa gona ba, a wani mataki na yakar matsalar yunwa da bunkasa tattalin arzikin matan dake jihar.

Shirin bayar da horon ya gudana ne ranar Alhamis 29 ga wata a garin Gombe bisa tsarin hadin gwiwa da ma’aikatar gona ta jihar da gidauniyar Hikima Foundation.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Wannan dai shi ne karo na farko da gwamnatin jihar Gombe ta kirkiro da wannan tsari, wanda kamar yadda aka tsara za a kara fadada shi ta yadda mata da dama dake jihar za su ci gajiyarsa.

Malam Usman Adamu darakta ne a ma’aikatar noma da kiwo ta jihar Gombe.

“Wannan taro yana da muhimmanci kwarai, taro ne wanda aka kira mata a matsayinsu na iyayen al’umma domin a koya musu wasu dabaru sabbi ta yadda za su iya yin noma a takaitaccen wuri da kuma ba tare da wasu matsaloli ba, kuma muhimmancin wannan taron kalubale irin na ruwan sama da karancin ruwa ba ya samunsa, da yake a cikin gida ne kuma kadan ne zai samar da abun da ake bukata a dan kankanen wuri.”

Ita Malama Rabi Salisu Musa tana daya daga cikin ma’aikatan dake aiki a ma’aikatar gona ta jihar Gombe, ta ce hakika an bar matan jihar a baya a harkar aikin noma wannan ne ya zaburar da gwamnatin jihar wajen shirya horon.

“Uwa ita ce malamar farko a rayuwa. Muna son yara da za su taso a nan gaba ya zama ba sai yaro ya je makaranta za a koya masa noma ba, ya tashi tun yana cikin gidan sa ya ga uwarsa tana yi, shi ne zai sa hankalinsa ya fara koya, idan ya tashi da son abun rashin aikin yi da ake samu na matasanmu maza da mata shi ma wannan zai tare mana.” (Garba Abdullahi Bagwai)