logo

HAUSA

Rundunar sojin Ukraine ta tabbatar da faduwar jirgin yaki na F16

2024-08-30 11:47:36 CMG Hausa

Rundunar sojin Ukraine ta tabbatar da faduwar jirgin yakinta na F16 yayin wani aiki a cikin kasar.

Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafin Telegram ta bayyana cewa, yayin da suke aiki, jiragen yaki na F16 sun lalata makamai masu linzami 4, kuma daya daga cikinsu ya bace lokacin da ya nufi aiki na gaba da zai gudanar.

Sanarwar ta kara da cewa, daga baya jirgin ya fadi kuma matukinsa ya mutu. Sai dai ba ta sanar da ainihin ranar da lamarin ya auku ba.

Ta kara da cewa, hukuma ta musammam ta ma’aikatar tsaron Ukraine na aiki a wurin yanzu haka, domin tantance musabbabin faduwar jirgin.

A farkon watan Augusta ne shugaban kasar Volodymyr Zelensky ya sanar da cewa, kashin farko na jiragen yaki na F16, sun isa kasar ta Ukraine. (Fa’iza Mustapha)