logo

HAUSA

Antonio Guterres ya yi kira ga Isra’ila da ta gaggauta tsagaita bude wuta a yammacin kogin Jordan

2024-08-30 11:09:16 CMG Hausa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga Isra’ila da ta dakatar da hare haren da take kaddamarwa a garuruwan yammacin kogin Jordan. Mista Guterres wanda ya yi kiran ta bakin kakakin sa Stephane Dujarric, ya ce ya damu matuka da halin da ake ciki a yankin, ciki har da batun munanan hare haren da sojojin Isra’ila suka kaddamar ranar Laraba a garuruwan Jenin, da Tulkarm da Tubas, wadanda suka kunshi hari ta sama, lamarin da ya haddasa kisan fararen hula, da lalata ababen more rayuwa da dama.

Stephane Dujarric, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema larabai a jiya Alhamis, ya ce babban magatakardar MDD ya yi Allah wadai da kisan fararen hula ciki har da yara kanana, yana mai cewa wannan lamari mai hadarin gaske dake wakana a yankin yammacin kogin Jordan, na kara tsananta yanayin da ake ciki a yankin yammacin kogin Jordan, yana mai fatan za a gaggauta tsagaita wuta nan take.

A cewar ofishin tsare tsaren samar da agajin jin kai na MDD, cikin kasa da kwanaki 2, hare haren dakarun sojin Isra’ila a garuruwan Jenin, da Tulkarm da Tubas, sun hallaka mutane 15, tare da jikkata wasu da dama.   (Saminu Alhassan)