Habasha na neman karin jari daga kasar Sin
2024-08-30 12:13:17 CMG Hausa
Gwamnatin kasar Habasha na kara karfafa gwiwar masu zuba jari daga kasar Sin, da su duba yiwuwar saka jarin su a yankunan masana’antu dake kasar, da ma yankin gudanar da cinikayya maras shinge irin sa na farko da aka kaddamar a Habasha.
Babban darektan kamfanin raya yankin masana’antu na kasar Habasha ko IPDC, mista Fisseha Yitagesu, da wasu manyan kusoshin gwamnatin kasar ne suka yi kiran, yayin taron bunkasa zuba jari da ya gudana a baya bayan nan, kamar dai yadda wata sanarwa da ofishin IPDC ya fitar a ranar Laraba ta bayyana.
Mista Yitagesu ya ce a halin da ake ciki, masu zuba jari daga kasar Sin ne ke da kaso mafi tsoka na jarin da aka zuba a yankunan masana’antun na kasar Habasha, wanda IPDC ke lura da su. Ya kuma jaddada muhimmancin jawo karin kamfanonin Sin zuwa yankunan masana’antu 13 dake Habasha, da ma sabon yankin gudanar da cinikayya cikin ‘yanci da aka kaddamar a Dire Dawa.
Wannan dai kira na neman zuba jari a Habasha, ya yi daidai da babbar manufar kasar ta inganta hadin gwiwa da Sin, da mayar da Habashan cibiyar sarrafa hajoji ta nahiyar Afirka.
Alkaluman baya bayan nan daga IPDC sun nuna cewa akwai daruruwan masu zuba jari na gida da na waje dake gudanar da hada hada a yankunan masana’antu na Habasha, da ma yankin gudanar da cinikayya cikin ‘yanci da aka kaddamar, wadanda da yawan su kamfanonin Sin ne suka kafa su. Wadannan cibiyoyi sun samar da guraben ayyukan yi na dindindin da na wucin gadi ga al’ummun Habasha su sama da 100,000 musamman ma matasa.
A baya bayan nan, gwamnatin Habasha ta gayyaci kamfanonin kera motoci masu aiki da lantarki ko EVs na Sin, domin su nazarci damammakin dake akwai na harhada irin wadannan ababen hawa a kasar. (Saminu Alhassan)