Me ra’ayin kare muhalli na kasar Sin ke kawowa duniya?
2024-08-30 15:13:39 CMG Hausa
A baya-bayan nan, wani jirgin ruwan dakon kaya dauke da motoci masu aiki da lantarki kirar kasar Sin ya je Jamus ya dawo. A baya, wannan jirgi na sufurin dubban irin wadannan motoci zuwa Spaniya da Birtaniya da Netherlands da Jamus da sauran wasu wurare, domin cimma karuwar bakutun kasuwannin kasashen. Kamfanonin kera motoci na kasar Sin sun ce cikin shekaru 3 masu zuwa, za su tura karin jiragen ruwa 6 zuwa 7 masu dakon ababen hawa, domin kayayyaki kirar Sin da suka dace da kare muhalli su shiga sassan duniya da inganta raya masana’antar sabon makamashi na cikin gida.
Karuwa makamashi mai tsafta a kasar Sin ba bunkasa samar da makamashin ya yi da ragewa duniya kudin da za a kashe wajen komawa amfani da makamashi mai tsafta ba, har da bayar da gagarumar gudunmuwa ga kare muhalli a duniya da tunkarar matsalar sauyin yanayi.
A matsayin kasa mai tasowa mafi girma, ba alkawarin daidaita fitar da hayakin Carbon da abubuwan dake zuke shi cikin kankanin lokaci kadai Sin ta yi ba, har ma da ci gaba da taimakawa duniya rage hayaki mai guba da inganta ganin dorewar makamashi mai tsafta a duniya. Nazari ya nuna cewa, kasar Sin ta zama wani tsani ga kokarin duniya na magance sauyin yanayi.
Yadda Sin ke yayata amfani da makamashi mai tsafta ba abu ne da wasu suke bukata ba, wani abu ne dake bukatar yunkuri, lamarin da ya cimma bukatun Sin na samun ci gaba mai inganci da ma cimma bukatun duniya, lamarin dake nuna sanin ya kamata a matsayinta na babbar kasa. (Fa’iza Mustapha)