logo

HAUSA

Shugaban Afrika ta kudu na fatan kara hadin kai da Sin a mabambantan bangarori

2024-08-29 14:17:11 CGTN Hausa

 

Shugaban kasar Afrika ta kudu Matamela Cyril Ramaphosa ya bayyana a jiya Laraba a Cape Town na kasar cewa, sabuwar gwamnatin kasar na fatan kara tuntubar Sin da zurfafa hadin gwiwarsu a bangarori daban-daban.

Jakadan Sin dake kasar Wu Peng ne ya gana da Matamela Cyril Ramaphosa a wannan rana, inda shugaban ya bayyana godiya ga taimakon da Sin ta dade tana baiwa kasarsa wajen raya tattalin arziki da al’umma, yana mai fatan za a cimma nasarar gudanar da taron dandalin tattauna kan hadin kan Sin da Afrika na shekarar 2024. Ya kuma kara da cewa, sabuwar gwamnatin kasar za ta ci gaba da nacewa ga manufar sada zumunta da Sin da ma fatan kara tuntubar kasar Sin da zurfafa hadin gwiwa a fannonin zuba jari da manyan ababen more rayuwa da sabbin makamashi da dai sauransu, ta yadda za a gaggauta inganta huldar kasahen biyu. (Amina Xu)