Sin ta gabatar da takardar bayani kan karkata ga nau’o’in makamashinta
2024-08-29 12:07:09 CGTN Hausa
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da wata takardar bayani a yau Alhamis, kan shirin karkata nau’o’in makamashin da kasar za ta rika amfani da su. Takardar ta nuna cewa, Sin na kokarin tabbatar da ra’ayin raya kasa tare da kare muhalli, da ma nacewa karkata ga hanyar samun bunkasuwa, tare da kara hadin gwiwa da al’ummar duniya, ta yadda za ta taka rawar gani irin nata wajen raya duniya mai kare muhalli. Matakin da kuma zai zama karfin jagoranci ga aikin karkata ga nau’o’in makamashi da duniya ke aiwatarwa.
Takardar ta nuna cewa, masana’antun sabbin makamashi na Sin sun baiwa duniya karfin samun bunkasuwa a wannan fanni. Sin ta samu bunkasuwa mai sauri a fannin sabbin makamashi ta dogaro da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha mai dorewa, da kyautatuwar tsare-tsaren samar da kayayyaki, da takara mai zurfi, da ma fifikon kasuwanni, wanda ya kara samar da hajoji ga duniya, da sassauta hauhawar farashin hajoji a duniya, matakin da ya taka rawa ga hadin gwiwar kasa da kasa wajen tinkarar sauyin yanayi, da amfanar al’ummar duniya.
Kaza lika, na’urorin samar da wutar lantarki ta amfani da haske rana, da iska, sun samar da sharadi mai kyau ga kasashe daban-daban, wajen samun bunkasuwar tattalin arziki bisa dogaro da wadannan makamashi. (Amina Xu)