Sin da Afirka aminai ne wajen neman zamanantar da kansu
2024-08-29 19:25:55 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau a nan birnin Beijing cewa, Sin da Afirka suna da ra’ayi daya kan neman zaman jin dadi, da hadin gwiwa, da zamanantar da kasa. Duk da cewa duniya na fuskantar sauyawar yanayi, Sin da Afirka sun kiyaye kasancewa abokai wajen yin kokarin zamanantar da kai tare.
Game da kasashen nahiyar Latin Amurka da dama da suka nuna kin amincewa da ayyukan Amurka na tsoma baki cikin harkokin cikin gidajensu, Lin Jian ya bayyana cewa, Sin ta nuna goyon baya ga kasashen Latin Amurka da su tabbatar da ikon mallakarsu, babu shakka manufar kama karya da siyasar ikon nuna karfi ta kasar Amurka ba za su samu dorewa ba.
Game da halin da Palesdinu da Isra’ila suke ciki kuma, Lin Jian ya bayyana cewa, Sin ta ki amincewa da daukar matakan tsananta yanayin, da yin Allah wadai da duk harin da aka kaiwa fararen hula. (Zainab Zhang)