Hukumar NEMA: Kusan mutane dubu 500 ne ambaliyar ruwa ya shafa a cikin wannan shekara a Najeriya
2024-08-29 10:10:35 CMG Hausa
Hukumar bayar da agajin gaggawa a tarayyar Najeriya, wato NEMA a takaice, ta tabbatar da cewa, ambaliyar ruwa da aka samu a sassan daban daban ya yi sanadiyar lalata filin noma kadada dubu dari da bakwai da dari shidda da hamsin da biyu.
Babbar daraktar hukumar Hajiya Zubaida Umar ce ta tabbatar da hakan ranar Laraba 28 ga wata lokacin da ta gabatarwa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa jadawalin rahoton adadin asarar da aka tafka sakamakon ambaliyar ruwa a wasu jihohin 31 na kasar, ta ce babu shakka ambaliyar ruwan za ta yi matukar shafar shirin samar da wadataccen abinci a kasa.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Shugabar hukuamr bayar da gaagjin gaggawar a tarayyar Najeriya ta ce, a kalla dai mutane dubu 500 ne ambaliyar ruwan ya shafa, inda daga cikin wannan adadi mutum 179 sun mutu, sannan kuma mutane 208, 655 ne suka kauracewa muhallansu, yayin kuma gidaje sama da dubu 80 kuma sun rushe.
Hajiya Zubaida Umar ta ce, hukumar tata ba ta da karfin da za ta iya shawo kan wadannan kalubale saboda karancin kudade.
“Babban kalubalen da muke fuskanta dai shi ne rashin wadatattun kudade. Wannan shi ne yake kawo wa hukumar cikas wajen aikin kai daukin gaggawa, haka kuma akwai batun rashin ingantattun kayayyakin more rayuwa wadanda suka hada da titunan mota, sau tari mu kan je jihohi, amma kuma ba ma iya kai daukin gaggawa yankunan da aka samu matsalar ambaliyar ruwa saboda rashin hanya. Matsalar ta biyu kuma ita ce rashin samun daidaituwa ta fuskar aiki a tsakanin masu ruwa da tsaki, wani lokaci idan mun je jihohi za mu tarar mutane da dama na yin aikin irin guda maimakon kowa ya dauki wani fanni na daban.” (Garba Abdullahi Bagwai)