Shugaban kasar Mali Assimi Goita zai halarci dandalin Sin da Afrika na FOCAC
2024-08-29 17:50:37 CMG Hausa
A jamhuriyyar kasar Mali, fadar shugaban kasar ta tabbatar da cewa, shugaban rikon kwarya, kanal Assimi Goita, zai halarci babban dandalin Sin da Afrika na FOCAC karo na 9, da zai gudana a Beijing tsakanin ran 4 da na 6 ga watan Satumba mai zuwa.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
A yayin wannan dandali, shugaba Assimi Goita zai jagoranci wata babbar tawagar kasar Mali, tare da burin karfafa dangantaka tare da kasar Sin a fannonin tsaro, tattalin arziki, gine-ginen ababen more rayuwa, noma da sauransu.
Harakar tsaro, na da babban tasiri ga kasar Mali, kuma wannan batu zai kasancewa a tsakiyar tattaunawa ganin yadda kasar take fuskantar kalubale da dama dake da alaka da kwanciyar hankali a shiyyar.
Haka kuma, a cewar fadar shugaban kasar Mali, halartar kanal Assimi Goita a wannan dandali na cikin tsari mafi girma na dangantaka tsakanin Sin da Afrika.
Wannan dandali da zai gudana a birnin Beijing a karkashin jagorancin shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai bayyana karara niyyar kasar Sin wajen tallafawa shirin zamanintar da Afrika.
A tsawon kwanaki uku na tattaunawa kan batutuwa kamar zamanintarwa, ci gaban masana’antu, zaman lafiya da tsaro, ilimi da kiwon lafiya.
Kuma a ranar 6 ga watan Satumba, taron masu masana’antu da kamfanoni na Afrika da Sin zai kasancewa muhimmin lokaci na wannan dandali, inda za a bullo da muhimman matakai dake manufar karfafa huldar tattalin arziki tsakanin Sin da Afrika. Kasar Sin ta zama kasa mafi zuba jari a nahiyar Afrika, tun yau da fiye da shekara 15, kasar Sin na taka muhimmiyar rawa wajen gina ababen more rayuwa da kafa kamfanoni.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.