Wakilin Sin ya yi kira ga dakarun kasashen waje da su kawo karshen zaman su a Syria
2024-08-29 10:31:52 CMG Hausa
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya yi kira ga dakarun sojin Isra’ila da su dakatar da kaddamar da hare-hare a Syria, kana sauran dakarun kasashen waje su kawo karshen haramtaccen zaman su a kasar.
Geng Shuang, ya yi kiran ne a jiya Laraba, yayin zaman kwamitin tsaron MDD da ya gudana game da batun kasar ta Syria. Yana mai jaddada muhimmancin martaba ikon Syria na mulkin kai, da kare alfarmar yankunanta.
Kazalika, ya yi kira ga daukacin sassan da batun kasar ya shafa da su kai zuciya nesa, su aiwatar da matakai na hakika don samar da daidaito tsakanin kasashen yankin, ciki har da Syria.
Har ila yau, ya bukaci manyan kasashe masu karfin fada a ji dake wajen yankin, da su taka rawar gani wajen sassauta yanayin da ake ciki a yankin. Geng ya tabbatar da cewa, Sin na goyon bayan kokari da wakilin musamman na MDD game da batun Syria mista Geir Pedersen ke yi, na ci gaba da aiki tare da dukkanin sassa karkashin jagorancin Syria, da manufofin kashin kanta, tare da fatan yin hadin gwiwa wajen cimma nasarar tsarin tattaunawar da ake yi, bisa salon tuntubar juna, da ganawa da bangaren gwamnatin kasar, matakin da zai haifar da cimma nasarar warware rikicin kasar ta hanyar siyasa. (Saminu Alhassan)