Adadin masu amfani da intanet a kasar Sin ya kai biliyan 1.1
2024-08-29 14:05:48 CMG Hausa
Wani rahoto kan ci gaban intanet a kasar Sin ya nuna cewa, daga karshen shekarar 2023 zuwa watan Yunin bana, adadin masu amfani da intanet a kasar ya karu da miliyan 7.42.
A cewar rahoton na cibiyar bayar da bayanan sadarwar intanet ta kasar Sin, sadarwar intanet ta kai ga kaso 78 na sassan kasar. (Fa’iza Mustapha)